Jirgin Solar Impulse 2 Mai Amfani Da Hasken Rana Kadai Ya Gama Zagayen Duniya

Jirgin saman nan mai amfani da hasken rana da ake kira Solar Impulse 2, ya zamanto jirgi na farko a tarihi da ya taba zagaye duniya ta hanyar amfani da makamashin hasken rana kadai.

Ranar Talatar da ta gabata ne jirgin da injiniyoyin kasar Swiss suka kera ya sauka a filin saukar jiragen sama na Abu Dhabi, wato inda ya tashi a farkon tafiyarsa domin zagaye duniya, wanda ya kwashe kimanin tsawon kilimita 40,000 ya kuma dauke shi tsawon shekara ‘daya.

Jirgin ya tsaya a kasashe 16 a fadin duniya kuma ba tare da amfani ko da digo ‘daya na Mai ba. A wata sanarwa da shugaban kamfanin da kuma direban jirgin suka fitar tace “burinmu yanzu shine mu ci gaba da baiwa mutane da kamfanoni da kuma gwamnatoci kwarin gwiwar su yi amfani da wannan fasahar a duk lokacin da ya kamata.”

Nauyin jirgin Solar Impulse bai fi nauyin motar hawa ba, amma yana da fuka fukai masu girman na jirgin sama Boeing 747. Yayi amfani da makamashin rana wanda kuma yake baiwa injinan jirgin masu karfi hudu, wadanda suke tafiyar da jirgin. Fuka fukan jirgin suna budewa har na tsawon mita 72 domin su zuko hasken rana.

Your browser doesn’t support HTML5

Jirgin Solar Impulse 2 Mai Amfani Da Hasken Rana Kadai Ya Gama Zagayen Duniya