A Yemen wani jirgin yaki da ba'a bayyana wanda yake iko dashi ba jiya Alhamis ya kai hari kan wata fadar shugaban kasar dake birnin Aden, bayan da sassa biyu masu gaba da juna suka fafata a tashar saukar jiragen sama da bashi da nisa da fadar.
Jami'an tsaro wadanda suke biyayya ga tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Sale sun kai hari kan babbar tashar saukar jiragen saman ta kasa da kasa dake Aden a safiyar jiya Alhamis, wanda ya janyo artabu da wasu mayakan sakai masu biyayya ga shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi, shugaban kasar wanda kasashen duniya suke goyon baya. Tilas aka rufe tashar saukar jiragen saman dalilin fadan da ake yi.
Haka nan kuma mayaka daga sassan biyu sun kuma gwabza a wasu sassan kasar.
Jami'ai sun ce an kashe dakaru hudu magoya bayan tsohon shugaban kasar da kuma mayakan sakai biyu daga banagaren shugaba Abd Rabbo. Akwai kuma wadanda suka jikkata masu yawa.
Wakilin Muryar Amurka daga sashen Somalia wanda yake Sana'a babban birnin kasar ya aiko da rahoton cewa jirgin da ya kai hari kan fadar shugaban kasar daga fadar kasar aka tuka shi zuwa Aden din, kuma magoya bayan shugaba na yanzu sunyi amfanin da makamai na harbo jirage kan jirgin bayan d a ya kaiwa fadar hari.
Wakilin Murya Amurka yace wani hadimin shugaban kasar yace "shugaban yana cikin koshin lafiya babu abunda ya taba shi".