Jirgin Kasa Ya Murkushe Shanu 52 A Kaduna

Shanu

A cewar rundunar 'yan sandan Kaduna labari mara tushe ne da suka samu ya sa makiyaya suka kada shanunsu bin layin dogon inda jirgin da ya taso daga Kaduna akan hanyarsa ta zuwa Abuja ya murkushe shanu 52

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce bayani mara tushe da Fulani suka samu ne ya sa suka kada shanunsu akan layin dogo wanda hakan ya yi sanadin murkushe shanu guda hamsin da biyu akan hanyar Kasarami zuwa Jere dake karamar hukumar Cukun.

Kwamishanan 'yan sandan jihar Malam Ahmed Abdulrahaman ne ya yiwa manema labaru bayani game da wannan hadari. Ya ce "Allah da ikon Sa suna tsakiyar gadar sai ga jirgi da ya taso daga Kaduna ya murkushe shanu 52 kuma dole jirgin ya tsaya saboda kasusuwan shanun sun shige cikin tayoyinsa abun da ya hanashi tafiya.

Yayinda 'yan sandan suka ruga wurin, inji kwamishanan 'yan sandan, "babu wani ta'addanci, hatsari ne Allah ya kawo shi". Ya ce Fulanin sun bi hanyar bisa jahlci ne da kuma da kuma yaudarar da aka yi masu na cewa babu jirgi ranar Lahadi. Kawo yanzu dai babu wani mutum da ya rasa ransa ko ya ji rauni.

Kwamishanan 'yan sandan Kaduna ya ce ya kira Fulani da manoma da matasa sun yi taron gaggawa inda ya kirasu su wayar da kawunan 'yanuwansu da ke kusa da layin dogon domin kada a sake barin shanu da sauran dabbobi ko manoma su bi hanyar jirgin

Akan matakin da hukumar dake kula da jiragen kasa da ke Lagos za ta dauka game da haduran da a ke samu akan layin dogo a kasar, Malam Yakubu Mahamud shugaban sashen hulda da jama'a ya ce a madadin hukumar suna bakin ciki kwarai akan hadarin da ya faru. Sun yi alhini da rasa rayukan dabbobin. A cewarsa tun ba yau ba suke ta yin shela da sanarwa a gidajen rediyo da talibijan cewa a dinga kiyayewa saboda jirgin na gudu sosai. Mutane su gujewa ketara layin ko bin kansa, musamman tsakanin Kaduna da Abuja.

Malam Yakubu Mahmud ya ce yanzu ma ana shirin gina katanga ta bulo domin a hana mutane ketara layin.

Dangane da biyan diya hukumar jiragen kasar ce za ta iya yanke shawara a cewar Malam Yakubu Mahmud.

Hukumar 'yan sanda ta kuduri anniyar yin taro da mutanen dake kusa da layn dogon tare da makiyaya da manoma. Haka ma ita hukumar jiragen kasan za ta kara fadakar da kawunan jama'a.

A saurari rahoton Isa Lawal Ikara

Your browser doesn’t support HTML5

Kaduna: Jirgin Kasa Ya Murkushe Shanu 52 - 3' 49"