Jirgin Farko: Yan Najeriya 182 Sun Dawo Gida Daga Afrika Ta Kudu

Yan Najeriya Da Suka Dawo Daga Kasar Afrika ta Kudu

Bayan da wani rikicin kyama da kin jinin baki ya barke a kasar Afrika Ta Kudu, hukumomin Najeriya sun dauki matakan dawo da yan kasarta gida daga kasar.

A kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na dawowa da ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu gida bayan harin kyamar baki da wasu ‘yan kasar ke yi akan su.

‘Yan Najeriya 182 ne su ka dawo gida a jirgin farko daya sauka a daren jiya a legas.

Shi dai wannan jirgi na kanfanin Air Peace da gwamnatin Najeriya ta tura domin daukan ‘yan Najeriya kimanin 650 da su ka nuna aniyar su ta dawowa gida, ance zai sauka legas ne da karfe 9 na safiya, a karshe dai jirgin ya sauka babban filin jirgin sama na kasa da kasa na murtala Mohammed ne da karfe 9:30 zuwa 10:00 na dare.

Ga dai abinda wani fasinja ke cewa bayan ya sauko daga jirgin, ya ce ana nuna wariya da kyamar baki a kasar Afirka ta Kudu, ‘yan kasar basa kaunar mu, basa kaunar baki.

Alhaji Idris Abubakar Mohammed shine babban jami’ain hukumar NEMA wanda su ka saka ido wajen tarbar ‘yan Najeriyan bayan saukar su a filin jirgin saman Murtala Muhammed.

Hukumomin Najeriya dai sun bayyana cewar an samu tsaikon dawowar ‘yan Najeriyan ne, a sakamakon matakin da jami’an hukumar shige da fice ta kasar Afirka ta Kudu su ka dauka da farko na sake tantance ‘yan Najeriyan domin sanin wadanda su ka shiga kasar ba bisa ka’ida ba, ko da yake daga bisani ance an samu masalaha.

Yanzu dai akwai ‘yan Najeriya kimanin 400 da suka rage a dawo da su gida, kuma watakila yawan nasu ya karu, ganin yarda ake ci gaba da samun rahotannin zaman dar-dar a tsaknin ‘yan Najeriyan da su ka yi sauran a kasar.

Saurari cikakken rahoton Babangida Jibril daga Legas:

Your browser doesn’t support HTML5

Jirgin Farko: Yan Najeriya 182 Sun Dawo Gida Daga Afrika Ta Kudu