Jiragen Yakin Syria Sun Auna Jerin Gwanon Motocin Sojojin Turkiya A Syria

Kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da hakan matuka, sannan ta ce harin ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla uku, baya ga raunata wasu 12.

Jiragen yakin Syria samfurin jet, sun auna akalla wata tawagar motocin sojin Turkiya da ta ketara cikin Syria jiya Litini, lamarin da ya kai ga rasa rayuka da jin raunuka.

Kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da hakan matuka, sannan ta ce harin ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla uku, baya ga raunata wasu 12.

Wani hoton bidiyo ya nuna yadda jiragen yakin Syria ke auna tawagar ta motocin sojojin Turkiyya, yayin da tawagar ke dosar garin Saraqeb da ke arewacin Idlib.

Ma’aikatar Harkokin wajen Syria ta koka da shiga cikin kasar ba izini da tawagar sojojin Turkiyyar ta yi.

Gidan Talabijin din gwamnatin Syria ya nuna cewa tawagar motocin na dauke ne da wasu kayan yaki don bai wa, a ta bakinsa, “wasu kungiyoyin ta’adda” da ke yakar gwamnatin Syriar a wajejen garin nan na Khan Sheikhoun mai muhimmanci.