Kasar Jamus da jihohin Oyo da Kano a Najeriya sun fara wani shiri da zai sa ido game da barkewar cututtuka tare da daukar mataikin gaggawa na shawo kan cututtuka idan an samu barkewar cututtukan.
Wannan shirin dai zai fara aikin ne a jihohin na Kano da Oyo, a matsayin mayakin farko, dai zai wanzu zuwa wasu jihohin Najeriya, bada dadewa ba.
Farfesa Gerrad Curius,yace sun zo jihar Oyo ne domin su duba yadda aikin zai fara aiki cikin nasara,kana su duba abubuwan da ake bukata a tanada dan aikin.
Shi kuwa Mr, Sylvester Ayina, mataimakin darakta a ma’aikatar kiwon lafiya ta Najeriya,wanda ya jagoranci tawagar Najeriya, yace za suyi aiki daga matakin kananan hukumomi har zuwa tarayya, yana mai cewa cututtukan da za’a saido akan sun hada da Cholera, murar Tsuntsaye da Ebola.