Shirin dai ya tanadi tallafawa namoma inganta harkokin noma da kuma kafa masana’antun sarrafa kayayyakin noman, ta yadda jihohin biyu zasu amfana.
Gwamnanan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yiwa wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin karin haske game da yarjejeniyar, inda yace sun tattauna da gwamnan jihar Lagos ta yadda zasu hada kai sun inganta harkar noma.
Dakta Abubakar Sadiq Gudugi, malami a sashen koyar da harkokin noma a jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida dake jihar Neja, yace idan har anyi wannan yarjejeniya da niyar taimakawa manoma su amfani to tabbas abu ne mai kyau.
Wannan dai ba shine karon farko ba da gwamnatin jihar Neja ke rattaba hannu domin inganta harkokin noma, ko a baya ma gwamnatin ta rattaba hannu da kamfanin Aliko Dangote, domin bunkasa harkokin noman Shinkafa da kuma Rake.
Saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5