Ranar 29 ga watan Agustan shekarata 1991 ne aka kirkiro jihar Taraba daga tsohuwar jihar Gongola, kuma jiha ce da ke da yawan kabilu shekaru 25 da suka gabata abubuwa da yawa sun wakana a jihar.
Wasu dai na ganin an samu ci gaba, yayin da wasu ke ganin ana tafiyar hawainiya, batun da jami’an gwamnatin jihar ke cewa ba haka zancen yake ba.
Wani bangare da ake ganin ya jawo koma baya a jihar shi ne na ‘kaurin sunan da jihar ta yi wajen tashe tashen hankula da ke da nasaba da kabilanci ko addini, batun da ya sa gwamnan jihar Darius Dickson Ishaku yin kira ga al’umomin da basa ga maciji da juna da akai zuciya nesa.
Sai dai kuma manazarta dai na hasashen cewa jihar na iya samun ci gaba a wasu shekaru 25 masu zuwa, muddin shugabanni da sauran al’umma za su yi watsi da abubuwan da suka hana jihar ci gaba a shekaru 25 da ta yi a yanzu.
Saurari wannan rahoton domin jin karin bayani dangane da wannan batu.
Your browser doesn’t support HTML5