Jihar Niger Ta Cika Shekaru 40 Da Zama Jiha

Jihar Niger dake Arewa maso tsakiyar Najeriya, ta cika shekaru 40 da zama ‘daya daga cikin jihohin Najeriya. A shekarar 1976 ne shugaban mulkin soja na wancan lokaci ya marigayi Murtala Ramat Muhammad, ya cire jihar Niger daga tsohuwar jihar Sokoto dake Arewa maso Yammacin Najeriya.

Tare da nada Murtala Nyako a matsayin gwamnan soja na farko a jihar Niger, ko da yake babu wasu bukukuwa na musammam da aka shirya domin jika shekaru 40 da haihuwar jihar, sakamakon matsalar rashin kudi da mahukuntan jihar suka ce suna fama da shi, amma akwai addu’o’I na musammam a masallatai da majami’ai domin nuna godiya ga Allah akan wannan rana.

Masu nazarin al’amura a jihar Niger dai sunce an sami ci gaba a wasu abubuwa na ci gaban jama’a, tsohon ma’aikaci a ma’aikatar yada labarai ta jihar Niger kuma basarake Jarman Minna, Alhaji Abdullahi Fayako, ya bayyana ci gaban da aka samu ta hanyar ilimi.

To sai dai a cewar Alhaji Shehu Musa Tanko, yace ci gaban da aka samu bai taka kara ya karya ba, bisa la’akari da jihohin da aka kirkiro a bayan jihar ta Niger.

Yanzu dai sabuwar gwamnatin jihar Niger tace tazo da kudirin yin gyara akan abubuwa da dama a cewar kwamishinan labarai da al’adu na jihar Mr. Jonathan Batsa. Kawo yanzu dai gwamnoni 14 ne suka mulki jihar, 9 sojoji 5 farar hula.

Saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Niger Ta Cika Shekaru 40 Da Zama Jiha - 3'35"