Sakataren yada labaran gwamnan jihar Dr Ibrahim Doba yace a lokacin da aka kafa kwamitin karbar mulkin jihar an nuna masu cewa gwamnatin Babangida Aliyu ta bar bashin nera miliyan dubu hamsin da bakwai.
Amma yanzu sun gano cewa akwai wasu abubuwa daban. Ta bakin Dr Ibrahim Doba yace tsohuwar gwamnatin ta ci bashi amma ta raba kudin tsakanin mukarabanta. Sun dauki bashin ne da sunan yin aiki dashi amma basu yi ba. Yace abun da zasu gaya masu shi ne suna son kudinsu. Su dawo da kudin.
To saidai tsohon sakataren gwamnatin jihar Alhaji Idris Ndako ya shaidawa Muryar Amurka cewa basu da damuwa akan duk wani bincike da za'a yi masu. Yace duk abun da suka sani sun sa a takarda. Duk abun da basu gane ba idan kuma sun yi niyyar abun da zasu yi su cigaba su yi. Yace shi a nashi matsayin bashi da wata fargaba.
Shi ma kakakin tsohon gwamna Babangida Aliyu, Mr. Israel Ebije yace suna shirye da duk wani bincike daga sabuwar gwamnatin. Yace idan suna son kafa kwamitin bincike su ci gaba.
Bisa ga alamu batun kudin na neman kawo takunsaka tsakanin sabuwar gwamnatin Abubakar Sani Bello da tsohuwar gwamnatin Babangida Aliyu.
A ranar Larabar da ta gabata sabon gwamnan sai da yayi wata ganawa ta siri da sarakunan gargajiyar jihar da ake harsashen taron nada nasaba da batun kudin da kuma harkokin tsaro.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5