Takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Neja mai barin gado da jam'iyyar APC mai jiran gado akan raba kujerun zuwa hajji na wannan shekarar.
Jam'iyyar APC ta fitar da wata sanarwa inda ta nuna rashin amincewa da yadda gwamnatin mai barin gado tayi saurin raba kujerun aikin hajji mai zuwa. To saidai ita gwamnatin ta musanta batun tana cewa ba haka lamarin yake ba.
Jonathan Batsa kakakin jam'iyyar APC wadda take shirin karbar mulki shi yayi korafin akan raba kujerun hajjin. Yayi zargin cewa gwamnati mai shudewa ta raba kujerun gaba daya duk da cewa sauranta makonni hudu ta mika mulki.
Batsa yana zargin wai wani rikici ne gwamnatin ta shirya masu. Wai kamata yayi gwamnati ta bar batun raba kujerun hajji ma sabuwar gwamnati. Jonathan Batsa ya shaidawa jama'a cewa da zara sun kama madafin iko zasu soke abun da gwamnatin yanzu ta yi. Wai zasu yi sabon tsari. Wanda suka ga ya cancanta shi zasu ba.
Amma a wani taron manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswar jihar kwamishanan kula da harkokin addinai Alhaji Shehu Haruna yace korafin APC bashi da tushe. Yace ko kujera daya ba'a raba ba. Wai ba'a ba kowa takarda ba. Yace idan sabon gwamna ya shigo yana son ya bayar da takardun wannan kuma ya rage gareshi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5