An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Neja Onarebul Adamu Usman tare da sauran shugabannin majalisar daga kan mukamansu.
'Yan majalisar 19 daga cikin 25 suka amince da saukar da shugabannin majalisar su guda hudu. To amma tun farko 'yan majalisar sun fuskanci turjiya daga jami'an 'yan sanda lokacin da 'yansandan suka yi kokarin hanasu shiga harabar majalisar.
Bayan sun tsige kakakin da sauran shugabannin sun zabi Onarebul Isa Kawu a matsayin sabon kakakin majalisar. Sabon kakakin ya bayyanawa Muryar Amurka dalilinsu na daukan matakin da suka dauka a daidai wannan lokacin.
To saidai Onarebul Adamu Usman wanda aka tsigen yace sam bai amince da tsigeshi ba kuma har yanzu shi ne kakakin majalisar. A fusace yace tsigeshi ya sabawa doka saboda babbar mai shari'ar jihar ta bada umurni kada majalisa ta tsigeshi.
Batun cewa kotu ta hana a tsigeshi Muryar Amurka ta tunawa Onarebul Adamu Usman cewa irin hakan ya faru da wasu 'yan majalisa biyu da kotu ta hana korarsu amma ya bujirewa umurnin, sai yace shi bai bujire ba domin a lokacin basu da takarda daga kotu.
Yanzu dai an rantsar da sabon kakakin majalisar wato tamkar majalisar tana da kakai biyu ke nan.
A wata sabuwa kuma yau majalisar a karkashin sabbin shugabanninta zata aikawa gwamnan jihar Mua'zu Babangida Aliyu takardar gargadin tsigeshi daga kan kujerarsa ta gwamna.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5