Jihar Nassarawa ta kaddamar da yaki da cutar kanjamau na tafi da gidanka

Ma'aikacin jinya yana bada shawara kan cutar kanjamau

Jihar Nassarawa ta kaddamar da shirin bada shawarwari da kuma gwajin cutar kanjamau na tafi da gidanka kyauta.

Jihar Nassarawa tare da hadin guiwar Babban Bankin Duniya, sun kaddamar da shirin bada shawarwari da kuma gwajin cutar kanjamau na tafi da gidanka kyauta, da nufin shawo kan yaduwar cutar.

Za a gudanar da shirin ne a kanannan hukumomin Lafiya da Akwanga da Obi da kuma Karu.

Wata jami’ar gudanar da shirin ta bayyana cewa, tawagar zata shafe kwana biyu tana aiki a kowacce daya daga cikin kanannan hukumomin hudu ta kuma yi kira ga al’ummar kananan hukumonin su ci moriyar shirin su san matsayinsu domin kare rayukansu da kuma na sauran jama’a.

Bisa ga cewarta, sai mutum ya san matsayinshi kafin ya dauki matakan da suka kamata ko neman magani ko kuma shawarwari. Mrs Eigege ta kuma bayyana cewa, akwai bukatar kara wayar da kan jama’a dangane da matakan kare kansu da kuma nuna wariyar da ake yiwa masu fama da cutar da yake hana wadansu sanin matsayinsu.

Rahoto na baya bayan nan ya nuna cewa, kashi 6.7% na al’ummar jihar Nassarawa suna dauke da kwayar cutar HIV. Abinda ya sa jihar kasancewa ta biyu da aka fi samun yawan masu dauke da cutar a Najeriya, bayan jihar Binuwe.