Asusun tallafawa kananan yara -UNICEF yana shirin hada hannu da kungiya mai zaman kanta “Service to humanity” wadda uwargidan gwamnan jihar Fatima Ibrahim Shema ta kafa.
Mataimakin wakilin UNICEF a Nijeriya dake da ofishi a Kaduna ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a masaukin gwamnoni dake a Kaduna tsakanin gidauniyar UNICEF da uwargidan gwamnan jihar Katsina.
Mataimakin wakilin UNICEF din Mr James ya bayyana cewar UNICEF zata kara karfafa hadin gwiwar ne da gidauniyar “service to humanity” na uwargidan gwamnan masamman ta fuskar samar da abinci mai gina jiki, da wayar da kan al’umma akan tsaftace muhalli da kuma harkokin rigakafi.
Mr James ya bayyana cewar UNICEF ta gamsu da irin kokarin da hadin gwiwar dake tsakanin kungiyoyin biyu cikin shekaru uku da suka wuce. Ya bada misali da aikin tattara bayanai akan marayu da yara marasa galihu da gidauniyar ta gudanar a jihar ta Katsina, inda aka gano dubban darurukan yara dake fuskantar matsaloli kuma suke samun tallafi daga kungiyoyin bada agaji irinsu “Save the children” dake tallafawa masu fama da karancin abinci mai gina jiki.
Jami’in ya kara da cewa aikin tattara bayanan ya taimakawa gwamnatin jihar Katsina a shirinta na kyautata jin dadin rayuwar al’umma a cikin sabon tsarin tallafawa almajirai wanda aka fito dashi ba da kwanan baya.
Akan lamarin tsutsar ciki kuma Mr James yace asusun UNICEF zai ci gaba da samar da tallafi kashi ashirin cikin dari na magani kamar yadda yayi alkawari tun farko. Sannan ya bukaci gwamnatin jihar ta Katsina da ta samar da kashi tamanin na maganin.
Tun farko uwargidan gwamnan jihar Katsinan Fatima Ibrahim Shehu Shema a nata jawabin ta bayyana cewar aikin tattara bayanai akan yara marassa galihu wanda gidauniyar “Service to humanity” ta gudanar tare da asusun UNICEF ya taimaka wajen samar da tallafi ga yara marassa galihu su fiye da dubu talati dake a jihar.
Uwargidan gwamnan ta alakanta nasarar da gidauniyar ta samu da tallafin da take samu daga asusun UNICEF da sauran kungiyoyi na agaji.