NASSARAWA: Mutane Dubu Talatin Zasu Sami Aiki A Kamfanin Dangwate

ma'aikatan hanyar Jirgin Kasa

Gwamnatin jahar Nasarawa tace kamfanin Siga da hamshakin dan kasuwannan Aliko Dangote ya kafa a yankin kudancin jahar zai ba mutane fiye da dubu talatin ayyukan yi.

Kamfanin wanda a yanzu ya share fili mai fadin hekta dubu sittin da takwas zai lakume kudi naira biliyan dari biyu da saba’in kamar yadda gwamnan jahar, Umaru Tanko Almakura ya shaidawa Muryar Amurka.

Sarkin manoman jahar Nasarawa, Alhaji Aliyu Usman yace dalibai da suka kamala karatu basu da ayyukan yi, zasu sami guraben aiki a kamfanin.

Basaraken gargajiya na yankin Awe, Alhaji Abubakar Umar na biyu yace jama’a da dama sun yi na’am da shirin don fiye da matasa dubu daya yanzu suna aiki a gonar, wanda an dauke su aiki kenan.

Ana sa nan da shekaru biyu zuwa uku kamfanin zai fara aiki tukuru.

Saurari rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Dangwate Zai kafa kamfanin siminti a Jihar Nassarawa-2:40"