Jihar Legas Ta Shiga Jerin Jihohin dake Da Man Fetur A Najeriya

Shugaba Muhammad Buhari da mataimakinsa

Shugaba Muhammad Buhari ya amince da saka jihar Legas cikin ayarin jihohin kasar dake da man fetur kuma zata dinga karbar kaso na musamman daga kudin kasa kamar yadda ake ba jihohin dake da man fetur.

Shugaban kwamitin tattara kudaden haraji na hukumar haraji ta kasa Alhaji Aliyu Muhammad shi ya tabbatarwa gwamnan jihar Legas Mr. Akinwumi Ambode amincewar shugaban kasa na saka jihar cikin ayarin jihohin dake da man fetur.

Alhaji Aliyu Muhammad yace daukan wannan matakin ya biyo bayan bincike ne da hukumar da sauran hukumomin gwamnati suka gudanar game da wasikar da gwamnatin Legas ta aikawa Shugaban Kasa Muhammad Buhari na bukatar a fara bata kashi goma sha ukku daga cikin dari na kudaden albarkatun man fetur na kasa a matsayinta na sabuwar jihar da za'a fara hakan man fetur a cikinta wannan watan.

A cewar shugaban kwamitin yanzu haka Shugaba Muhammad Buhari ya amince a fara baiwa gwamnatin jihar ta Legas kashi goma sha ukku cikin dari na kudaden harajin da za'a samu daga albarkatun man fetur da wani kamfanin Legas mai suna Folawuyo Oils zai fara hakowa.

Malam Garbadeen Muhammad kakakin kamfanin man fetur na kasa ko NNPC yayi karin haske akan tasirin da wannan zai yiwa tattalin arzikin jihar Legas da ma kasa baki daya. Arzikin man fetur na kasa ne kuma zai karawa kasar arzikinta. Baicin karin kudi da jihar zata samu ba za'a samu fashe fashen butuntun mai kamar na Niger Delta ba.

Su talakawan Legas sun yi murna da samun man a jiharsu amma suna rokon gwamnati ta rage masu kudin mai da kuma inganta rayuwarsu.

Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Legas Ta Shiga Jerin Jihohin dake Da Man Fetur A Najeriya - 3' 32"