Jihar Kano Ta Sake Bude Makarantar Dakta Hassan Gwarzo Bayan Lalata Dalibai

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Game da fasadin din da ya faru a makarantar sakandaren Dr. Hassan Gwarzo da ke jihar Kano na zargin aikata luwadi da daliban makarantar, rundunar ‘yan sanda ta gabatar da mutane 4 a gaban kotu da suka hada da Farfesa Ibrahim Ayagi, da Shugaban makarantar Malam Muhammad Bashir.

Sai kuma wasu ma’aikatan gadi a makarantar wato Kabiru Saidu da Ado Umar. Bugu da kari a cikin tuhumar da ‘yan sanda ke yiwa Farfesa Ayagi har da na kokarin sabawa da’a da dattaku. Wannan cajin laifuffuka sun hada da na aikata badala a cikin al’umma.

Tun ranar Talata data gabata ‘yan sandan na Kano suka gabatar da laifuffuka shida ga wadanda ake tuhumar, amma sai a ranar alhamis ta maida adadin laifuffukan da ake tuhumarsu zuwa guda takwas da kuma wasu caji guda biyu akan mai makarantar shi kadai.

A daya bangaren kuma gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwar sake bude makarantar don ci gaba da karantun yaran. Kamar yadda gwamnatin ta shaida shine ta bude makarantar ne saboda kar a ci gaba da ajiye daliban makarantar ba tare da ci gaba da karatunsu ba.

To sai dai ga dukkan alamu wannan matakin na gwamnatin Kano bai yiwa iyayen yaran da abin ya shafa ba, inda suka bayyanawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari cewa, ba su goyi bayan wannan matakin ba, musamman yadda aka kirasu gidan gwamnati a baya aka musu alkawarin bi wa ‘ya’yansu hakkinsu.

Alkalin da ke shari’ar Abba Abubakar Kabara ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Fabrairu mai zuwa na shekarar nan, don ci gaba da bin Kadin wannan matsala da kuma jin ko kotun zata amince da karin tuhummar da ‘yan sandan suka yi. Ga rahoton Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Kano Ta Sake Bude Makarantar Dakta Hassan Gwarzo Bayan Lalata Dalibai - 3'17"