Gwamnatin tarayya ta sha alwashin yin aiki kafada da kafada da jihohi domin samar ma 'yan Najeriya ingantattun hanyoyi da gidaje kamar yadda ministan ayyuka Babatunde Fashola ya bayyana a birnin Jos fadar gwamnatin Filato.
Ministan yana rangadin dubawa da tantance hanyoyin gwamnatin tarayya.
Ministan ya bukaci kungiyar gwamnonin Najeriya su kafa wata doka a jihohinsu kan yadda mutane zasu yi anfani da hanyoyi bisa kan ka'ida.
Yayinda yake ganawa da gwamnan Filato Simon Lalong ministan ya bukaceshi da su sa ido domin cimma burin samarda hanyoyi ingantattu wa al'umma.
Minista Fashola yace manyan motoci na wulakanta hanyoyi da nuna halin ko in kula lamarin da kan janyo munanan hadura dake sanadiyar hasarar rayuka da dama.
Da yake mayar da martani gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya tabbatar samar ma ma'aikatar takardaar mallakar filaye domin gina rukunin gidaje da gwamnatin tarayya ke shirin yi a jihohi. Yace jihar ashirye take ta samar da filayen da gwamnatin tarayya ke bukata. Gwamnan ya kuma kira gwamnatin tarayya ta biya jihar kudaden da gwamnatin Jang ta kashe wajen gina hanyoyin gwamnatin tarayya a jihar.
Ga karin bayani.