A cikin hirarshi da shirin Domin Iyali, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Mohammed Garba yace rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa ya nuna cewa, akwai alamar aukuwar abinda ake zargi ya faru a wannan makaranta ta Dr Hassan Gwarzo, kuma an dade ana wannan abu a makarantar. Dalili ke nan da suka bada shawara cewa, bai kamata a bude makarantar yanzu ba.
Kwamishinan yace shawarar da kwamtin ya bayar cewa a ci gaba da rufe wannan makarantar manuniya ce cewa, abinda ake zargi ya faru a wannan makaranta. Bisa ga cewarshi, abinda ya sa ba a fito kiri kiri ance an kama wannan makaranta da wannan zargi ba, shine, domin akwai kwamiti na hukumomin tsaro da aka kafa wanda shima yake gudanar da bincike kan wannan lamari. Saboda haka majalisar zartaswa ta jihar Kano tace ya dace kafin a fito a yanke hukumci kan wannan batu, ya kamata a jira rahoton kwamitin.
Gwamnatin jihar Kano ta kuma ce zata kashe naira miliyan arba’in da dubu dari uku da ishirin kan wajen tura daliban makarantar Dr Hassan Gwarzo dake ajin karshe domin su rubuta jarabawar kamala makarantar sakandare. Sai dai daukar wannan matakin bai kwantawa wadansu mutane ba, inda masu kungiyoyin farar hula suka ce, ba a yiwa talakawa adalci ba, idan za a dauki kudin da ya kamata a yi masu aiki wajen biyawa “’Yan gata” a maimakon tilastawa makarantar aman kudin da daliban suka riga suka biya.
A nasu bangaren, lauyoyin dake bin diddigin wannan batun sun bayyana cewa, tun farko sun san cewa, gwamnati bata yi niyar bin Kadin wannan laifin ba. Domin tunda farko sunce kamata ya yi aba cibiyar da ya kamata ta gudanar da bincike amma ba gwamnati ta kafa kwamiti ba, daga nan ta koma tana jiran sakamakon binciken jami’an tsaron da ya kamata tun farko sune ya kamata a dankawa wannan hakin.
Ga cikakken rahoton da Mahmoud Ibrahim Kwari ya hadawa shirin Domin Iyali.
Your browser doesn’t support HTML5