'Yan-bindigan da su ka afka makarantar ta St. Albert tsakanin karfe 7:30 zuwa 8:00 na yamma bayan cin abuncin dare sun bude wuta inda su ka dunga harbe-harbe kafin sace daliban makarantar guda uku.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN reshen jahar Kaduna Rabaren John Joseph Hayeph ya ce wasu daliban da su ka yi gudun ceton rai ma sun ji raunika.
Wannan hari dai na zuwa ne daidai lokacin da gwamnonin Arewa maso yamman su ka sanya wasu dokoki na bai daya, sai dai masani kan harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai nakasu game da wadannan matakai.Tuni dai 'yan-bindigan da su ka sace daliban makarantar ta St. Albert su ka kira iyayen su don tattauna kudin fansa, inji shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a jahar Kaduna, Rabaren John Joseph Hayeph.
Dama dai rundunar 'yan sandan jahar Kaduna ta tabbatar da sace daliban har ma mai magana da yawun rundunar ASP Mohammed Jalige ya ce jami'an tsaro sun bi sahu.
dalilin-da-ya-sa-aka-kasa-shawo-kan-matsalar-tsaro-a-arewacin-najeriya---masana
adamawa-yan-bindiga-sun-kori-yan-sanda-daga-ofishinsu
an-kashe-wani-an-sace-wasu-uku-a-wata-majamiar-kogi
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5