Jihar Florida Na Shirin Fuskantar Guguwar Micheal

Guguwar Michael

Mahaukaciyar guguwa da aka ba lakabi da suna Michael ta kara samun karfi zuwa ma'aunin karfin guguwa na uku mafi tsanani, yayinda ta tasarwa zirin shakatawa na Panhanle a jihar Florida.

Hasashen yanayi yace guguwar Michael zata zo da iska mai tsananin karfi tafiyar kilomita 195 a sa'a daya kuma zata isa gabar tekun Golf da safiyar yau Laraba.

An bada kashedin mahaukaciyar guguwar a yankin iyakar jihohin Alabama da Florida dake gabashin kasar. Ana sa ran za a samu iska da ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu wurare.

Gwamnan Florida Rick Scott ya bayyana guguwar Michael a matsayin mummunar guguwa, kuma ya yi kashedi cewa guguwar zata iya yin barna a wasu wurare a cikin jihar. Ya gargadi mazauna jihar da su bi umarnin ma ‘aikatan ceto kuma su maida hankali ga labarai.

Shima shugaban Amurka Donald Trump yace ma'aikata ceto na tarayya sun zama a cikin shiri.