Kakakin rundunar tsaro ta jihar Filato Keftein Ikedichi Iweha ya bayyanawa Muryar Amurka musabbabin wannan sabon harin da aka kai.
Ranar 17 ga watan uku yace sun samu rahoton cewa Fulani makiyaya sun rasa shanu dari hudu. Yace a lokacin sun ba makiyayan hakuri da yin alkawarin zasu taimaka a gano shanun. Sun kokarta har sun gano shanu 282 to amma Fulanin sun hakikance sun san inda aka kai shanun. Kokarin da Fulanin suka yi su kwato shanun da kansu ya kaiga fada har Fulanin suka rasa mutane hudu.
Inji Keftein Iweha wannan sabon harin tamkar ramuwar gayya ne daga su Fulanin. Yace sun yi bincike kuma sun gano cewa Fulanin dama can sun rantse sai sun rama duk da hakurin da lallashin da aka bayar aka kuma yi masu. Yace sun samu labarin cewa makiyaya dake yankin duk sun tashi kwansu da kwarkwatarsu kafin akai hari na baya bayan nan. Rundunar tsaro ta shiga wuraren kuma tana cigaba da zakulo wadanda suka ji rauni tana kaisu asibiti. A nashi kidayar yace mutane goma sha daya ne suka rasu.
To saidai hukumomin karamar hukumar suna da nasu bayanin da adadin wadanda suka rasa rayukansu.Mai ba karamar hukumar Barkin Ladi shawara akan labarai Peter Matong yace adadin wadanda aka kashe ya wuce 11 kamar yadda sojoji suka sanar. Yace a kauyen farko a kashe mutane 15 kana a kauye na biyu an kashe mutane 12, wato duka an kashe mutane 27 ke nan.
Batun cewa an saci shanu Peter Matong yace babu gaskiya a batun.Yace abun da ya faru shi ne da Fulani suka shigo kiwo dauke da makamai sai mutane suka tunkaresu sai suka gudu suka bar shanunsu. Yace mutane sun tara shanun sun ba hukuma. Maganar satar shanu bata kan gaskiya.
Shi kuma shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Filato Haruna Boro Useini cewa ba Fulani ne suka kai harin ba saboda wai , basu da wata damuwa da mutanen yankin. Yace a saninsa an samu shanu kuma suna murna. Yace kabilun Birom su suka taimka aka samu shanun. Sabo da haka yace babu yadda zasu tashi su kai masu hari kuma.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5