Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, ta tarayyan Najeriya, Gernot Rohr, yace ba zai canza jerin sunayen tawagar ‘yan wasa 23 da suka fafata da kasar kamaru a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za'ayi a kasar Rasha, ba
Tawagar Najeriya tabi Kamaru har gida ta yi kunnen doki 1-1 a wasan rukunin (B) Gernot Rohr, ya bada tabbacin zai amfani da wadannan ‘yan wasan a wasan da Najeriya za ta yi da kasar Zambiya, shima na neman tikitin kofin Duniya,
A ranar Asabar 7, gawatan Oktoba 2017 a matakin wasan rukuni, a filin wasa na Uyo, dake jihar Akwa Ibon, a tarayyar Najeriya, inda yanzu hakan Najeriyar, ce take kan gaba a rukunin na (B) da maki Goma a wasanni 4 da aka gwabza, sai kuma kasar Zambiya, wacce take biye da ita da maki bakwai a mataki na biyu.
Kasar Kamaru, wacce tuni aka cire ta a neman tikitin tana mataki na ukku ne da maki ukku, Kungiyar kwallon kafa ta Algeriya, ta na mataki na hudu ne a rukunin da maki daya.
Kasa daya ce zata samu tikitin zuwa gasar a rukuni rukuni inda ake da rukuni har biyar, kuma idan Najeriya, ta samu nasara a wasan da za ta yi da kasar Zambiya to ya tabbata cewar ita ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya, a wannan rukuni na (B) domin zai zamo ita tafi kowace kasa yawan maki a rukunin.
Ga jerin sunayen da aka fidda a matsayin wadanda zasu fafata da kasar Zambiya, a wannan ranar, Masu tsaron Raga akwai Daniel Akpeyi, Ikechukwu Ezenwa, Ayodele Ajiboye,
Masu tsaron Gida sune,
William Troost-Ekong, Abdullahi Shehu, Leon Balogun, Elderson Echiejile, Uche Agbo, Chidozie Awaziem, Ola Aina,
Sai ‘yan wasan tsakiya wadanda suka hada da John Mikel Obi, Ogenyi Onazi, Wilfred Ndidi, Oghenekaro Etebo, John Ogu, da Mikel Agu,
Acikin jerin ‘yan wasan gaba kuwa akwai
Ahmed Musa, Kelechi Iheanacho, Moses Simon, Alex Iwobi, Odion Ighalo, Victor Moses, sai Anthony Nwakaeme
Sai wadanda suke jiran ko ta kwana wato (Standby) sune Dele Alampasu, Tyrome Ebuehi, Aaron Samuel, Afeez Aremo, da kuma Ifeanyi Ifeanyi.
Your browser doesn’t support HTML5