Dan wasan baya na tsakiya na kasar Argentina, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, na Kasar Spain, mai suna Javier Mascherano, dan shekaru 33, da haihuwa, ya bayyana ra'ayinsa na rataye takalminsa na wasan kwallon kafa wa kasarsa ta Argentina, amman sai bayan an dawo daga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara 2018, wadda za'ayi a kasar Rasha.
Dan wasan ya ce yin haka ya zamo dole domin subar wa matasa masu tasowa damar suma su bada irin tasu gudumawar ga kasar.
Javier Mascherano, ya dade yana takawa Argentina, leda inda ya fara da kungiyar matasa ‘yan kasa da shekaru 20, a shekara 2003-2004, sai na ‘yan shekaru 23, daga 2004-2008 daga bisani ya shiga tawagar manyan ‘yan wasan kasar ta Argentina.
Ya buga wasanni har guda 139, wa kasarsa ta Argentina, inda ya jefa kwallaye uku a wasannin daban daban, dan wasan ya fafata wasanni a kungiyoyi kwallon kafa da dama a nahiyoyi daban daban,
A yanzu dan wasan yana taka leda a kungiyar kwallon kafa na Barcelona, na kasar Spain, inda nan ma ya buga wasannin har 200 ya kuma jefa kwallo daya kacal a raga.
Kasar Argentina tana daya daga cikin kasashe 22 da suka samu gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 2018, da zai wakana a kasar Rasha inda a satin da ya gabata ta lallasa kasar Ecuador, daci 3-1.
Your browser doesn’t support HTML5