Fitaccen jarumin Hollywood Michael K. Williams wanda ya taka rawar Omar Little a fim din “The Wire” ya rasu. Shekarunsa 54.
An tsinci Williams ne a mace a gidansa da ke yankin Brooklyn a New York a ranar Litinin.
‘Yan sandan birnin New York na binciken mutuwar jarumin akan yiwuwar ya sha kwayar da ta wuce kima a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Williams, ya kasance jarumin da ya fi fice a fim din na “The Wire” wanda kamfanin HBO ya watsa daga 2002 zuwa 2008.
Baya ga fim din na “The Wire” Williams ya fito a wasu manyan fina-finai irinsu “Boardwalk Empire” wanda shi ma kamfanin HBO ya watsa a tsakanin 2010 zuwa 2014, sai “Twelve Years a Slave,” da kuma “Assasin’s Creed.”
Amma rawar da ya taka a matsayin Omar, ita ta hasakaka tauraronsa, kamar yadda ya taba fada a hirar da aka yi da shi a shirin Stephen Colbert “The Late Show’” a 2016.
An haifi Williams a shekarar 1966 a Brooklyn, mahaifiyarsa daga yankin Nassau take a Bahamas, mahaifinsa kuma mutumin kudancin California ne. Ya yi karatunsa a makarantar George Westinghouse.
A karon farko da ya shiga harkar nishadantarwa, Williams ya fara fitowa ne a matsayin dan rawa a wakokin Missy Elliot, Ginuwine, Crystal Waters da kuma Technotronic.