Jarumin Kannywood Umar Yahaya Malumfashi ‘Ka Fi Gwamna’ Ya Rasu

Marigayi Alhaji Umaru Yahaya Malumfashi (Ka fi Gwamna)

An yi sallar jana’izarsa a unguwar Hotoro da misalin karfe 9 na safe a birnin Kano.

Allah ya yi wa jarumin masana’antar Kannywood, Alhaji Umaru Yahaya Malumfashi wanda aka fi sani da “Ka Fi Gwamna” ko kuma “Bankaura” rasuwa.

Jarumin ya rasu ne a daren ranar Talata a jihar Kano da ke arewa maso yammcin Najeriya bayan fama da rashin lafiya.

“Za a yi jana’izarsa a unguwar Hotoro da misalin karfe 9 na safe.” In ji jarumi Abba Almustapha, wanda ya wallafa wani tsohon hotonsu da marigayin.

A ‘yan kwanakin nan bayanai suka yi ta bayyana cewa Malumfashi, wanda ya taka rawa wajen kayatar da ‘yan kallo a shirin “Kwana Casa’in” mai dogon zango na fama da rashin lafiya.

“Ina bakin cikin sanar da rasuwar abokin aikinmu Umar Yahaya Malumfashi, wanda aka fi sani da Ka fi Gwamna ko kuma Bankaura.

“Ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalansa da kuma masana’antarmu ta Kannywood baki daya.” In ji jarumi Alhaji Sani Mu’azu, wanda suka fito tare a shirin na Kwana Casa’in.

"Allah ya ji kan ka Baba Alhaji Umar Bankaura. Allah ya ji kan ka ya maka rahama." In ji jarumi Ali Nuhu.