Jarumin Hollywood Donald Sutherland Ya Mutu Yana Da Shekaru 88

Obit Donald Sutherland

Jarumi Kiefer Sutherland ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Cikin alhini ina sanar da ku mutuwar mahaifina, Donald Sutherland.”

Donald Sutherland, jarumin fina-finan Hollywood, wanda a tsawon lokaci da ya yi yana aikinsa ya yi fina-finai da suka hada da “The Dirty Dozen” da The Hunger Game,” ya mutu, kamar yadda dansa ya bayyana a ranar Alhamis.

Jarumi Kiefer Sutherland ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Cikin alhini ina sanar da ku mutuwar mahaifina, Donald Sutherland.”

Dattijon na da kamanni na musamman, sannan nutsattse ne, wanda ya taka rawan gani a fina-finan da ya yi fiye da rabin karni.

Da yake mika sakon ta’aziyyarsa Firai Mininstan Canada Justin Trudeau, ya ce jarumin da ya lashe kyautar Emmy da Golden Globe yana da basira ta musamman.

Ya shaida wa wani taron manema labarai cewa “Na sami dama a lokacin da nake karami don saduwa da Donald Sutherland, har ma a matsayi na na saurayi, wanda ba shi da cikakkiyar masaniya na basirar Donald Sutherland, ina matukar alhini da mutawar tauraron.”

Ya ce “shi mutum ne da ke da kwarjini sosai, mai hazaka a cikin sana’arsa, kuma babban jarumi a Canada, sannan za’a yi kewarsa sosai.”

Shi ma da yake mika sakon ta’aziyyarsa shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana daya daga cikin jarumai wanda ya nushadantar da duniya a cikin gomman shekaru.