Jarumar "Desperate House Wives" Za Ta Tafi Gidan Yari

Jaruma Felicity Huffman

Jaruma Felicity Huffman

Wata kotu a birnin Boston da ke jihar Massachusettes a Amurka, ta yankewa fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayon nan Felicity Huffman, hukuncin zaman gidan yari na tsawon kwanaki 14.

An yanke mata hukuncin ne bayan da aka same ta da hannu a wata almundahanar ba da cin hanci domin a samawa 'yarta gurbin karatu a daya daga cikin fitattun kwalejojin Amurka.

Kotu har ila yau ta umurci jarumar, wacce ta taka rawa a fim din Desperate House Wivesda ta biya dalar Amurka 30,000 sannan ta yi aikin al’uma na tsawon sa’o’i 250.

Huffman dai ta amsa laifin ba da cin hancin dalar Amurka 15,000 domin a karawa diyarta makin da zai ba ta damar shiga daya daga cikin manyan kwalejojin Amurka.

Ita ce ta farko da aka yankewa hukunci cikin iyaye 51 da ake tuhuma da hannu a wannan almundahana.