Shugaba a fannin siyasa na Majalisar Dinkin Duniya, ta ce matsayar da aka cimma ta nukiliyar Iran na cikin “tsaka mai wuya” bayan da Amurka ta janye daga wannan yarjejeniya a watan da ya gabata.
A cewar Rosemary DiCarlo, mai kula da harkokin siyasa a majalisar, Sakatare Janar, ya nuna takaicinsa matuka, kan wannan koma-baya da aka samu kan matsayar ta nukiliyan Iran, wacce aka cimma a shekarar 2015 wacce kuma ake wa lakabi da Joint Comprehensive Plan of Action ko kuma “JCPOA” a takaice, tana mai cewa, kamata ya yi a tunkari matsalolin da ke tattare da matsayar ba tare da an nuna son zuciya ba.
DiCarlo ta bayyana hakan ne, a taron farko da aka gudanar na kwamitin sulhu na majalisar, kan yadda ake aiwatar da wannan yarjejeniya, tun bayan ficewar Amurka a ranar 8 ga watan Mayu, inda ta ce sau 11, hukumar IAEA ta kasa-da-kasa mai sa ido kan fasahar makaman kare dangi, ta ba da tabbacin cewa Iran na bin ka’idojin da aka gindaya mata.