Mai shari’a Kolawale ya janye ne daga shari’ar saboda nuna damuwa ga yadda lauyan hukumar EFCC, Ofem Uket ya ki barin ayi wa wani mai bada shaida tambayoyi.
Hukumar EFCC ta shigar da karan da zargin ofishin Sambo Dasuki ya bayar da kwangilar da ta shafi ruwan sha ga wani jami’in soja Kanal Nicolas Ashinze, da ta kai Naira Biliyan uku da Miliyan ‘dari.
Lauyan Ashinze dai yayi tambaya da a nuna masa inda sunan wanda yake karewa ya fito a kwangilar, ko kuma idan akwai korafin rashin gudanar da kwangilar daga ma’aikatar ruwa ko kuma babban banki wanda ya biya kudin.
Jaridar Daily Sun ta rawaito cewa Alkali Kolawale ya mayar da kundin shari’ar ga shugaban babban kotun tarayyar Abdul Kafarati.
A cewar ‘dan jarida Sani Tashir, wannan ganin cewa bai kamata ba lauyan dake wakiltar hukumar EFCC bai kamata ya nuna irin wannan ‘daliba a kotu ba, ganin yadda Alkali ke kokarin janyo hankalinsa.
Shari’ar Sambo Dasuki dai na daga cikin shari’o’in dake jan lokaci, da ba mamaki ma hakan ya sanya babban Alkali Walter Onnoghen, bullo da hanyar sauraron shari’un cin hanci da rashawa a takadirin lokaci.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5