Tchiani ya jaddada anniyar majalisar CNSP da ta gwamnatin rikon kwarya wajen karfafa dankon zumunta a tsakanin Najeriya da Nijar wadanda ya ce ‘yan uwan juna ne.
Matakin da masana sha’anin diflomasiya ke ganin zai zama mafarin yayyafa ruwa a wutar rikicin da ya taso sanadiyyar kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Wasikar wacce tun a ranar 29 ga watan Satumba shugaban majalisar soja ta CNSP Janar Abdourahamane Tchiani ya saka wa hannu, ta shigo hannunmu manema labarai a yammacin Litinin 2 ga watan Oktoba.
Jagoran sojojin juyin mulkin na mai cewa ina farin cikin isar da sakon taya murnar zagayowar wannan rana ta 1 ga watan Oktoba zuwa gareka da gwamnatinka da al’ummar Najeriya.
Zan kuma yi amfani da wannan dama da sunana da na majalissar CNSP da gwammantin don jaddada anniyarmu ta bada hadin kai a dukkan yunkurin karfafa hulda da ci gaban dangantaka da dan uwantakar dake tsakanin kasashen nan namu 2 da al’umominmu.
Janar Abdourahamane Tchiani a wannan wasika ya bayyana fatan ganin gwamnatocin kasashen biyu wato Najeriya da Nijar masu makoma guda za su samar da hanyoyin shayo kan kowane irin sabanin da ya tasowa a tsakaninsu domin tabbatar da ci gaban zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.
Dangantaka ta yi tsami a tsakanin hukumomin Najeriya da Nijar sakamakon juyin mulkin da soja suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum a karshen watan Yulin da ya gabata.
Yayin da majalisar CNSP ke cewa bakin alkalami ya bushe shugaban Rikon CEDEAO Bola Ahmed Tinubu da takwarorinsa na kasashen kungiyar sun ce ba za ta sabu ba.
Sun nemi da a mayar da hambararen shugaban kasa kan kujerarsa mafari kenan aka yi ta kai ruwa rana.
A halin yanzu da aka yi haka masana sha’anin diflomasiya irinsu Moustapha Abdoulaye na kallon wannan yunkuri na hukumomin Nijar a matsayin wanda ka iya bude hanyar zama kan teburin sulhu.
Wata wasikar taya murnar ta daban da Shugaban Majalisar CNSP ya rubuta ita ce wacce ya aike wa jagoran sojojin juyin mulkin kasar Guinea Conakry kanal Mamadi Doumbouya a albarkacin bikin ranar samun ‘yancin kai karo na 65 da aka gudanar a wannan a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba.
Janar Tchiani ya jinjina wa hukumomin Guinea saboda goyon bayan da suka bai wa Nijar a washegarin barkewar rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Har ma wasu rahotanni na cewa Nijar ta halarci bikin faretin na kasar Guinea ta hanyar wata tawagar jami’an kasar da aka aika takanas.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5