Janar CG MUSA Bai Mutu Ba - Rundunar Tsaron Najeriya

 Babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Janar CG Musa

Babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Janar CG Musa

Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta yi watsi da jiya-jitar cewa babban hafsan Hafsoshin tsaron kasar, Janar CG MUSA ya mutu.

Yau ne dai wata jaridar da ake bugawa a yanar Gizo ta wallafa rahoton mutuwar babban kwamandan mayakan kasar.

Kakakin rundunar tsaron Najeriyar, Brigadiya Janar Tukur Gusau ya yi bayanin cewa jita-jitar nan ba gaskiya ba ne kuma Janar CG Musa ya dawo Najeriya daga bulaguron aiki da ya kai kasashen waje.

Tuni kuma babban Hafsan ya isa ofishinsa yau da safe don ci gaba da ayyukan sa kamar dai yadda ya saba.

Saboda haka rundunar tsaron Najeriyar ta yi tir da wannan rahoto na kanzon kurege da jaridar ta buga inda ta ce ko kadan babu sanin yakamata a cikinsa.

Don haka ta nemi manema labaru su rinka bincikar gaskiyar labari kafin su wallafa.