Wannan shirin dai zai fara aiki ne a jihohin Oyo da Kano a matsayin matakin farko da zai wanzu zuwa wadansu jihohin Najeriya a nan gaba ba da dadewa ba.
Daya daga cikin wakilan kasar Jamus, Profesa Jerid Kurias da ya jagoranci tawagar kasar Jamus zuwa jihar Oyo domin fara shirin ya bayyana cewa, sun je jihar Oyo ne domin neman hanyar fara aiwatar da shirin ba tare da bata lokaci ba, da kuma gudanar da bincike da nufin ganin shirin ya yi nasara.
A nata bayanin daya daga cikin wakilan gwamnatin Jamus, Dr Gabriela ta bayyana cewa, sa ido zai taimaka wajen shawo kan barkewar cututukan da kuma maganinsu.
Cututukan da za a sawa ido sun hada da kwalara, cutar Ebola, murar tsuntsaye da dai sauransu. Za a gudanar da aikin ne ta wajen amfani da wayar salula ta zamani.
Ga rahoton da wakilinmu Hassan Umaru Tambuwal ya iko mana.
Your browser doesn’t support HTML5