Jam'iyyun Kawance a Gwamnatin Nijar Sun Kare Kasafin Kudin 2018

Shugaban kasar Nijar Isssoufou Mahammadou

Jam'iyyun kawance da ke mulkin kasar Nijar sun fito fili sun goyi bayan shirin kasafin kudin shekarar 2018 na gwamnati duk da cewa lamarin har yanzu yana jawo cece-ku-ce daga jam'iyyun adawa da kungiyoyin kare hakkin jama'a.

A karon farko kawancen jam'iyyun da ke mulkin kasar Nijar sun bayyana matsayinsu a hukumance dangane da tsarin kasafin kudin shekarar 2018 wanda har yanzu yake haifar da ta da jijiyoyin wuya.

A cewar kungiyoyin da ke adawa da shirin, kasafin zai jefa talakawan kasar cikin wani kuncin rayuwa mai tsanani.

Su ma jam'iyyun adawa sun danganta shirin da zama daidai da rashin sanin mulkin kasa.

Sai dai Shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya, Bazoun Muhammad, ya ce su ma sun san akwai wurare kalilan da aka samu tsadar wasu abubuwa amma ba yadda 'yan adawa ke cewa ba.

Ya ce basu rage albashin ma'aikata ba ko rage ma'aikatan ko kuma amshe masu albashi.

Bazoum ya ce, lokaci ne ya zo mai tsananin wuya, shi ya sa aka kara haraji akan wutar lantarki da sauransu.

Matakin jibge sojojin kasashen yammacin turai a wasu sassan Nijar domin yaki da ta'addanci na cikin abubuwan da ke shan suka daga 'yan adawa da wasu kungiyoyi.

Akan sojojin waje da ke kasar, Bazoun Muhammadou ya ce su nufinsu shi ne 'yan Nijar su kwanta lafiya.

A saurari rahoton Suley Barma da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyun Kawance a Gwamnatin Nijar Sun Kare Kasafin Kudin 2018 - 3' 07"