Jam'iyyar Republican Ta Ayyana Donald Trump A Matsayin Dantakara

Jam'iyyar Republican ta ayyana hamshakin dan kasuwan nan mai harkar gine-gine Donald Trump, a matsayin dan takararta na Shugaban kasa a hukumance, a zaben da za a yi wannan shekarar ta 2016.

Jiya Talata, rana ta biyu a babban taron jam'iyyar a Cleveland na jahar Ohio, wakilan zaben na delegate sun gabatar da kuri'un jahohinsu daya bayan daya, wanda ya sa Trump, wanda sabon shiga ne a siyasa, ya samu kuri'u 1,237 da ya ke bukata don zama dan takarar.

Dan takarar ya ce, "Zan yi aiki tukuru kuma ba zan bashe ku ba!" wannan ne sakon da Trump ya gaggauta aikawa ta kafar Tweeter bayan da aka gama gabatar da kuri'un.

Zai buga da 'yar takarar Democrat mai jiran ayyanawa, tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, a babban zaben da za a gudanar ranar 8 ga watan Nuwamba don maye gurbin Shugaba Barack Obama, wanda zai sauka a watan Janairun badi.