Jam'iyyar PDP Zata Shiga Zaben Kananan Hukumomi A Kano

Ibrahim Shekarau tsohon gwamnan jihar Kano wanda ya canza sheka zuwa PDP

Yayin da lokacin zaben kananan hukumomin jihar Kano ke karatowa, jamiyyar PDP tace babu ja da baya zata shiga zaben.
A wani jawabi da yayi wa manema labarai, tsohon gwamnan jihar Kano wanda ya fice daga APC zuwa PDP Mallam Ibrahim Shekarau, yace jam'yyarsu zata shiga zaben kananan hukumomin jihar Kano da za'a gudanar.

Yace jam'iyyarsu ba zata ja da baya ba. Yace "abun da suke gabatarwa shi ne koke-koke akan wasu dabaru da suka gani ana yi na kwan gaba, kwan baya, da hukumar zaben keyi. Sun rubuta takarda zuwa ga shugaban hukumar zaben dangane da abun da suka lura yana faruwa. Idan anyi ba dai-dai ba, zasu nuna inda aka yi hakan. Abun da suka yi akai, shine zai haifar da irin abubuwan da zasu yi."

Alhaji Sani Hassan Hotoro, yace "jam'iyyar APC da gwamnatin jihar Kano, da hukumar zabe sun hana jam'iyyarsu takara a wasu wuraren, amma an amince wa jam'iyyar APC ta tsaya a duk kananan hukumomin, duk da cewa kawo yanzu bata tsayar da 'yan takararta ba."

Alhaji Ismaila Idris Garba, kwamishanan yada labarai na hukumar zaben jihar yace sun samu takardar korafin jam'iyyar PDP. "Jam'iyyar na son a kara mata lokaci domin a cewarta ba zasu iya karbar takardar da zasu cika ba ranar uku ga watan Afrilu, kana a ce su cika ranar, su kuma mayarda ma hukumar zaben hudu ga wata ba. Ranar hudu ga watan hudu ya kamata su rufe amma har ranar basu rufe ba. Ba zasu yi masu wata alfarma ba, domin ko za'a yi masu sau goma, ba zasu shirya ba. Duk jam'iyyar da ta karbi takardar cikawa, zata yi zabe koda ma jam'iyya daya ce."

Alhaji Ismaila ya kara da cewa ba zasu kara koda sa'a daya ba domin abun yana son ya zama "wasan yara".

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar PDP Zata Shiga Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano-2' 55"