Jam’iyyar PDP Tace Ana Neman Murkushe Ta Da Sauran Yan Adawar Najeriya

PDP

Babbar Jam’iyyar adawa ta Najeriya ta fitar da sanarwar nuna rashin gamsuwa ga yadda tace gwamnatin Buhari na yaki da Almundahana, dai dai lokacin da hukumar EFCC tayi awon gaba da mataimakin shugaban Jam’iyyar Uche Secondus, bisa tuhamar wata babbar badakala.

Takarda daga jami’in Shari’a na Jam’iyyar Barista Victor Yusufu Kwon, tace gwamnatin ta APC na neman murkushe PDP ne da sauran ‘yan adawar kasar. Kwana daya kenan da mika ragamar Jam’iyyar ga sabon shugaba Modu Sharif, tsohon mukaddashi Secndus ya fada hannun EFCC.

Tuni mukaddashin amintattun Jam’iyyar Walid Jibrin yace ba ‘yan PDP bane kadai su kayi zarmiya ba a Najeriya, ya ci gaba da cewa idan an kama dan Jam’iyyar PDP da laifi kuma aka kai shi kotu wannan zai hana PDP n rayuwar ta ne. yace ba PDP bace tayi wannan lalatar ba wasu ‘yan PDP ne, idan hakane to abi gaskiyar al’amurra da dokokin zai kai kowa ga hukunci.

Shi kuma Ciroman Bakan Daura, wanda yake na hannun damar shugaba Buhari na ganin matakin ya dace, inda har ya zargi Jam’iyyar PDP da kwashe kudaden Najeriya tun daga kananan hukumomi zuwa gwamantin Tarayya. Har ma yace sunyi haka ne da niyya domin su hada Buhari da talakawan Najeriya.

PDP dai tace tana ganin nan gaba shugabannin ta da suka hada da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawan Godswill Obot Akpabio zasu fuskanci irin wannan kamun. In za a tuna kakakin PDP Olise Metuh na zaman beli ne bisa tuhumar badakalar Naira Miliyan 400, wanda har ya kai shi ga zaman wakafi a gidan yarin Kuje.

Domin karin Bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam’iyyar PDP Tace Ana Neman Murkushe Ta Da Sauran Yan Adawar Najeriya - 2'58"