Jam’iyyar PDP Ta Ce Babu Wani Ci Gaba Da Aka Samu a Jihar Neja

PDP

Yayin da gwamnatin APC ke cika shekaru biyu da hawa kan karagar mulki a Najeriya, babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Neja ta ce babu wani ci gaba da aka samu ta fuskar gudanar da ayyukan raya ‘kasa a jihar.

Gwamnatin APC dai ta ce ta gudanar da ayyuka da dama da za a ayi alfahari da su a cikin shekaru biyun da ta kwashe akan mulki.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Neja, Barista Tanko Beji, ya ce a gwamnonin wasu jihohi na gayyato mutane domin a kaddamar da ayyukan da aka yi, amma a jihar Neja babu wani aiki da aka yi balle kuma a kaddamar.

Haka zalika wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, ya ji ta bakin wasu mutanen karkara akan cikar gwamnatin APC shekaru biyu kan mulki. Alhaji Abdurra’uf, daga karamar hukumar Agwara, yace sun ji dadin ziyarar da mai girma gwamna ya kai musu, da kuma gyara musu hanya da yayi.

Shi kuma, Abdurrahman Mohammad direba Agwara, cewa yayi a baya sun sha fama da matsaloli na Asibiti wadanda ke ci musu tuwo a kwarya, amma gwamnati ta yi kokarin shawo kan matsalar, sai dai kuma har yanzu suna bukatar a sake duba lamarin.

A daya bangaren kuma, shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar Neja, Injiniya Mohammad Imam, yace gwamnatin APC ta samu ayyuka da ba a kammala su ba, wanda yanzu haka baki ‘daya an kammala su, domin ci gaban jihar baki ‘daya.

Sai dai kuma har yanzu babu alamun gwamnatin jihar Neja ta shirya wani bikin cika shekaru biyu akan karagar mulkin.

Domin karin bayani ga rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam’iyyar PDP Ta Ce Babu Wani Ci Gaba Da Aka Samu a Jihar Neja - 3'07"