Jam'iyyar Democrat ita ce ta fara tsayar da dan darikar Katolika a matsayin dan takarar shugaban kasa a lokacin da amurkawa ke dari dari da masu bin darikar.
WASHINGTON DC —
Jam'iyyar ce kuma ta fara tsayar da bakin mutum a matsayin dan takarar shugaban kasa wato, Barack Obama, har ya ci zabe sau biyu a jere.
Jiya jam'iyyar ta kara tarihi kan tarihi a siyasar Amurka inda a karon farko a tarihin kasar, mace ta samu isassun kuri'u da suka sa ta zama 'yar takarar shugaban kasar Amurka.
A zaben fidda gwani da aka yi jiya a nan Amurka, ko tantama babu, Hillary Clinton tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka, kuma matar tsohon shugaban kasar, Bill Clinton, ta lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat. Yanzu ita ce zata tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar a zaben watan Nuwamba mai zuwa.
Your browser doesn’t support HTML5