Jam’iyyar CPDM Mai Mulkin Kamaru Ta Yi Zabe

  • Ibrahim Garba

Shugaban Kamaru, Paul Biya

Jam'iyyar CPDM mai mulkin kasar Kamaru ta fara shirye-shiryen zabukan 2018 tun daga yanzu, ta wajen zaben sabbin shugabanni.

Jam’iyyar CPDM mai mulki a Janhuriyar Kamaru ta yi babban taronta na “congre,” inda ta zabi sabbin shugabannin shiyya-shiyya da gundumomi da kananan hukumomi da karkara. Wannan zaben sharar fage ne ga babban zaben da za a yi a shekarar 2018.

Kamar akasarin sauran zabukan Afirka, wannan zaben na cike da korafe-korafe da zarge-zargen magudi da sauransu. Misali, wakilnmu ya ce a mazabar Douala ta Biyu, wato Unguwar Hausawa, inda wani matashi mai suna Alhaji Muhammadu Yakubu, wanda y ace tun dama sun san za su ci zabe saboda shugabannin baya sun kasa tabuka abin a zo a gani.

To amma wani dan jam’iyyar adawa ta UMS Mai Masara, mai suna Alhaji Sani Janga y ace ga dukkan alamu jam’iyyar CPDM Mai Masara ta kama hanyar wargajewa.

Ga wakilinmu Garba Awwal da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Jam’iyyar CPDM Mai Mulkin Kamaru Ta Yi Zabe - 2'47''