Jam’iyyar APC Reshen Jihar Neja Ta Kori Sanatoci 3 Da Yan Majalisu 6 Daga Jam’iyyar

APC

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Neja, ta sanar da korar Sanatoci guda 3 Neja da kuma yan majalisar wakilan Najeriya guda 6 daga cikin jam’iyyar ta APC.

Taron manema labarai ne jam’iyyar APC ta kira, inda sakataren jam’iyyar a jihar Neja Barista Muhammad Liman, yace sun dauki matakin ne saboda yan majalisar da kuma Sanatocin, sun kasa biyan kudaden haraji na jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar APC ya tanada.

Sakataren tsare tsare na jam’iyyar APC a jihar Neja, Alhaji Isma’ila Modibo, yayi karin haske kan wannan batu inda yace da akwai haraji na jam’iyya da ake biya wata uku uku, ya kuma ce an zabi yan majalisun kusan shekara guda kenan, jam’iyya ta rubuta musu takarda kan su biya wannan haraji amma har yanzu wasu basu biya ba, hakan yasa doka ta tanadi cewar sun fita daga jam’iyyar.

Sai dai kuma wakilin Muryar Amurka Mustapha Batsari, yayi kokarin jin ta bakin Sanatocin da aka kora amma abin ya ci tura, sai dai ya samu jin ta bakin wasu yan majalisar Wakilai. Hon. Abubakar Lado, wanda yake daya daga cikin mutanen da jam’iyyar tace ta kora. Yace bai san inda suka sami wannan doka ba a tsarin jam’iyyar, kuma basu da hurumin dakatar da su a jam’iyya koda kuwa sun aikata laifi ne.

Shima dai Hon. Shehu Sale Rijau, ya mayar da martani inda yace tatsuniyarsu ce kawai, ba wani Sanata da za a ce an kora.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam’iyyar APC A Jihar Neja Ta Kori Sanatoci 3 Da Yan Majalisu 6 Daga Jam’iyyar - 2'48"