Jam'iyyar Democrats ta sami nasarori a zaben gwamnoni da aka yi jiya Talata anan Amurka.
Dan jam'iyyar Democrat Ralph Northam ya sami nasara a zaben Gwamnan jahar Virginia, a zaben da babu tabbas kan makomarsa, ya doke dan jam'iyyar Republican Ed Gillespie, a zaben da zai maye ko cike gurbin gwamnan jahar dan Democrat Terry McAuliffe.
Northam wanda ahalin yanzu shine mataimakin gwamnan jahar ta Virginia yana kan gaba a yawancin kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a, kamin abokin takararsa Ed Gillespie ya fara tallace tallace inda yake sukar Northam kan batutuwa da suka hada da 'yan banga,batun bakin haure da kuma kare mutum-mutumi a zaman kayan tarihi.
Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ahalin yanzu yake ziyarar aiki a yankin Asia, ya bayyana goyon baya ga Gillespie a jiya Talata, amma nan da nan ya canza lafazi bayan da Gillespie ya fadi. Yana cewa ta shafin Twitter cewa, Ed Gillespie yayi aiki tukuru, amma bai rungumi shi Donald Trump da batutuwa da yake goyon bayan su ba.
Haka nan a jihar New Jersey ma, dan jam'iyyar Democrat Phil Murphy, kamar yadda aka zata, ya doke mataimakiyar gwamnan jahar ta New Jersey Kim Guadagno, a takarar da aka zabi wadda zai maye gurbin gwamnan jahar dan Republican Chris Christie mai barin gado.