Gobarar ta tsahi da missalin karfe Shida da rabi na yammacin ranar Asabar wadda ta rika ci har zuwa safiyar Lahadi. Bayanai na nuni da cewa gobarar ta lashe dakin karatu na matsugunnin dindindin a jami’ar da bangaren koyon ilimin halayyar jama’a wato Sociology da sashen kimiyyar siyasa da sashen koyon halin tunanin dan Adam da dai sauransu.
A cewar shugaban sashen fasaha na jami’ar Farfesa Tor Irabor, jami’ar Jos ta tafka asarar da dole sai kasashen duniya sun taimaka mata. Shima mataimakin shugaban sashen hulda da ‘dalibai na jami’ar cewa yayi babban abin damuwa shine sakamakon jarabawar ‘dalibai da suka kone kurmus.
Yayin da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta ziyarci Jami’ar, ta tarar da ‘dalibai musamman wadanda ke karatu a sassan da suka kone suna ta tafka kuka da yin nadamar yadda lamarin ka iya shafar rayuwarsu.
A halin da ake ciki kuma shugaban jami’ar Jos Farfesa Sebastian Maimako, a wata sanarwa ya aikawa manema labarai ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda yace suna kan bincike don sanin musabbabin tashin gobarar da irin asarar da jami’ar ta tafka.
Saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5