Yayinda jami’an ‘yan sanda ke fama da rashin samun albashi, daya daga cikinsu da yake Dapchi a jihar Yobe ya bara saboda ya bugawa Muryar Amurka waya ya bayyana halin da suke ciki.
Jami’in da ya nemi a sakaya sunansa yace rashin samun albashi da alawus na Nera dubu daya kowace rana da ya kamata a biyasu saboda inda suke aiki, wato wajejen ‘yan ta’addan Boko Haram, ka iya haddasa koma baya ga aikin tsaro.
A cewar jami’in alawus dinsu na tun watan daya babu wanda ya samu ko kwandala kama daga su dake jihar Yobe har zuwa wadanda suke jihar Borno. Wasunsu sun yi wata uku, hudu ba’a biyasu albashi ba. Suna fama da rashin kudin biyan bukatun iyalansu da ma na yau da kullum. Ya kira gwamnati ta tuna dasu ta yi masu adalci.
Maganar ta kai ga kunne babban sifeton ‘yan sandan Ibrahim Idris wanda ya ba jami’in kula da kudi na rundunar ‘yan sanda ya binciki dalilin dake sa albashin ‘yan sanda ke makalewa a ofishin akantan Najeriya cikin sabon tsarin biyan albashi.
Bala Ibrahim mai taimakawa babban sifeton ya ce a gayawa kakakin rundunar ‘yan sanda cewa matsalar ba a wurinsu take ba. Matsala ce da take da asali a ma’aikatar kudi. Malam Bala Ibrahim ya ce ba dede ba ne a tura mutum daji wurin aiki yana shan rana amma kuma aki biyansa hakkinsa.
A cewar Bala, babban sifeton ‘yan sandan ya yi barazanar kai kara wurin shugaban kasa muddin ma’aikatar kudi bata biya jami’ansa ba. Ya tura jami’insa mai kula da harkokin kudi ya tare a ma’aikatar kudi ta san yadda zata biya jami’ansa.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya domin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5