Fiye da mutane 100 ake tsare da su a Vietnam bayan da aka gudanar da wata zanga zangar nuna kyamar wata doka da ake kokarin kafawa akan wasu kasuwanni na musamman da ake son kirkirowa wadanda mutane da yawa ke tsoron zasu fi fifita ‘yan kasuwan China fiye da na ‘yan kasar ta Vietnam.
Masu zanga zangar sun jefa duwatsu da bama bamai hadin gida, a kan hedkwatar karamar hukumar dake kudancin tsakiyar lardin Binh Thuan. Kafar yada labaran kasar mai suna VN Express ta ce mutane 102 aka kama kuma ‘yan sanda da dama sun raunana a lokacin da sukai arangama da masu zanga zangar.
Ha’ila yau, an gudanar da zanga zangar a wadanzu biranen Vietnam da suka kunshi Ho Chi Minh da Hanoi.
Dokar da ake kokarin kafawa dai zata bai wa ‘yan wadansu kasashen damar hayar filaye a yankuna masu tattalkin arziki na musamman guda uku har na tsahon shekaru 99. Nuna bacin ran talakawan Vietnam ne ya sa ‘yan majalisar dokoki suka jinkirta tabbatar da dokar, har suka daga maganar amincewa da ita zuwa karshen wannan shekarar.