Litinin din nan, jami'an tsaron kasar Yamal suka harbe masu zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati talatin da daya a Sana'a baban birnin kasar, a ci gaba da mumunar tarzomar tun watan Maris da aka fara tada kayar bayar kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Ali Abdullah Saleh.
A birnin Ta'iz dake kudancin kasar kuma an kashe mutum hudu da raunana mutane arba'in a arangamomin da aka yi litinin din nan.
A birnin Sana'a kawai, sojojin gwamnati sun kashe mutane hamsin da bakwai da raunana mutane dari shidda da hamsin tun ranar lahadi, lokacinda sojojin dake biyaya ga gwamnatin kasar suka bude wuta akan dubban masu zanga zangar.
Mumunar murkushe masu zanga zangar ta hadasa musayar harbe harbe tsakanin sojojin dake goyon bayan shugaba Saleh da wadanda ke biyaya ga Janaral Ali Mohsen Al Ahmar, wanda ya canja shekara ya koma bangaren masu hamaiya a yan watanin da suka shige. Yanzu haka birnin Sana'a yana rabe tsakanin sojojin Janaral Almar da suka bale da kuma sojojin dake biyaya ga gwamnatin kasar.
Litinin din nan matasa masu zanga zangar suka fadada yankin sansanin zanga zangar da suke yi zuwa wani yanki dake kusa da gidan iyalin shugaba Saleh akan hanyar data doshi fadar shugaban kasa. Rundunar sojan Janaral Ahmar daga baya itama ta kutsa wannan yanki.
Ma'aikatan jakadanci da yan siyasar kasar kuma suna ta kokarin farfado da shirin mika mulki daya cije. Shirin daya tanadi shugaba Saleh ya mika ragamar mulki. Wakilin Majalisar Dinkin duniya Jamal bin Umar da kuma sakataren kungiyar hada kan kasashen yankin guda shidda, Abdul Latif Al Zayani, litinin suka isa birnin Sana'a, kuma ana sa ran suma zasu halarci tattaunawar da ake yi.
Har yanzu dai shugaba Saleh yana can birnin Riyadh kasar Saudi Arabiya inda yake murmurewar daga rauni daya ji a harin da aka kaiwa fadarsa a watan Yuni.