Jami’an tsaro a birnin Maiduguri dake arewacin Najeriya suna neman maharan da suka kai hare haren bom da kuma bindigogi jiya lahadi da suka yi sanadin kashe mutane 10.
Jami’an tsaro a birnin Maiduguri dake arewacin Najeriya suna neman maharan da suka kai hare haren bom da kuma bindigogi jiya lahadi da suka yi sanadin kashe mutane 10. Kwamandan rundunar tsaro ta hadin guiwa a Maiduguri yace maharan sun kai hari a wani gidan saida barasa kusa da barikin ‘yansanda, mako guda bayan hare haren boma bomai uku da aka kai a wani gidan barasa da yayi sanadin mutuwar mutane 25. Majo janar jack Nwaogbo yace babu wanda ya dauki alhakin harin na jiya lahadi, wanda ya hada da kashe wani dan siyasa na jam’iya mai mulki a jihar Borno. Ana kyautata zaton kungiyar addinin Islama mai tsats-tsauran ra’ayi Boko Haram ce ke da alhakin kai hare haren. Kungiyar ta kai hare haren bom, da kisan gilla da yin kwantan bauna da kuma fasa gidajen yari a arewacin Najeriya cikin ‘yan shekarun nan. Kungiyar Boko Haram bata amince da kundin tsarin mulkin Najeriya ko gwamnatin tarayya dake Abuja ba, ta kuma ce zata ci gaba da yaki sai an kafa kasa mai cin gashin kanta karkashin dokar musulunci. Shugaba Goodluck Jonathan ya yi tayin tattaunawa da kungiyar, amma kawo yanzu kungiyar tayi watsi da wannan tayin, da cewa, ba zata tattauna da gwamnati ba yayinda jami’an tsaro suke kokarin murkusheta. Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta kama aiki cikin wannan makon tare da sake zaben da dama daga cikin tsofaffin ministocinsa. Parfesa Abubakar Umar kari na jami’ar Abuja ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram ce babbar kalubalar dake gaban gwamnatin. Yanzu haka Boko Haram a matsayin akida da kuma kungiya tana barazana ba ga harkokin tsaro a Najeriya kadai ba, amma har da ci gaban kasancewar kasar daya. Tare da ci gaba da kaiwa wadanda ba Musulmi ba hare hare da kungiyar ke yi a gidajen barasa, Kari yace, yana yiwuwa kungiyar ta fuskanci tankiya da kuma ramuwar gayya a kasar da kungiyar kare hakin Bil’adama Human Right Watch tace an kashe a kalla mutane 800 a rikicin addinin da aka yi a kasar wanda ya biyo bayan zaben shugaba Goodluck Jonathan. Sanarwar da darektan jami’an yansandan ciki na jihar Borno Ahmed Abdulhameed ya bayar a rubuce na nuni da cewa, wadansu ‘yan siyasa na fakewa da kungiyar Boko Haram wajen gudanar da miyagun ayyuka.