Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Nijeriya Sun Kama Mutane 100 Da Ake Zargin 'Yan Tsattsauar Kungiyar Islama Ne


Harin da 'yan Boko Haram su ka kai kwanan baya a Nijeriya
Harin da 'yan Boko Haram su ka kai kwanan baya a Nijeriya

Hukumar ‘yan sandan ciki a Nijeriya ta ce ta damke sama da mutane 100 da ake zargin ‘yan kungiyar Islama mai dauke da makami

Hukumar ‘yan sandan ciki a Nijeriya ta ce ta damke sama da mutane 100 da ake zargin ‘yan kungiyar Islama mai dauke da makami da ke arewacin Nijeriya din nan ne, da wasu jiga-jiganta.

Jami’an hukumar basu ambaci sunan kungiyar ba, to amman kungiyar Boko Haram kan dau alhakin kai munanan hare-hare a jihohin arewacin Nijeriya shida, ciki har da kashe-kashen gilla da kuma hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda. Hare-haren sun hada da harin bam da aka kai a watan jiya kan hedikwatan ‘yan sanda Nijeriya da ke Abuja.

Ma’anar Boko haram dai it ace, “Ilimin Yammacin Duniya Haramun Ne.” Kungiyar na son ta wanzar da shari’ar Islama a arewacin Nijeriya.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi tayin tattaunawa da kungiyar, to amman ya zuwa yanzu kungiyar ta ki.

‘Yan sanda a birnin Maiduguri na arewacin Nijeriya na farautar wadanda su ka kai jerin harbe-harbe da hare-haren bam das u ka halla mutane 10 ranar Lahadi.

Babu dai wanda ya dau alhakin kai harin to amman ‘yan sanda na zargin ‘yan Boko Haram.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG