Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ruwaito cewa, an kwantar da akalla mutane 6 a asibiti sakamakon harbin bindiga bayan taho mu gamar a Brazzaville babban birnin kasar.
A ranar Lahadi mai zuwa ne kasar zata kada kuri’ar kan kwaskwarimar sabon kudurin kundin tsarin mulkin kasar, wadda za ta rushe wa’adin mulki 2 na shugaban kasa da kuma kayyade shekarun dan takarar shugabancin kasa ba zasu haura saba’in ba.
Kakakin ‘yan adawa da yunkurin kwaskwarimar Tsomambet Anaclet, ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa, karon arangamar ranar Talatar ya fara ne a lokacin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar da suke kokarin taruwa.
Shedun gani da ido sun ce, ‘yan sandan sun buga barkonon tsohuwa tare da bude wuta da bindiga. Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa a ranar hanyoyin sadarwar ta internet ba sa aiki a mafi yawancin sassan birnin.