Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kongo Zata Tono Gawarwaki 400 da Ta Binne a Kabari Guda


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasar Kongo ta tono gawarwakin mutane 400 da ta binne a kabari guda a gudanar da bincike saboda a gano dalilin mutuwarsu

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahunkuntar kasar jamhuriyar demokaradiyyar Kongo da su tono gawarwakin nan har su 400 da suka binne a rami guda kusa da Kinshasa domin gane dalilin mutuwar su

Jamiaan kasar na Kongo suka ce a kalla gawarwaki 421 ke cikin ramin, kuma na yara ne kanana ne wadanda yawanci marasa matsugunni ne.

Sai dai shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar ta Congo Jose Maria Aranaztace yana da matukar muhimmaci asan dalilin mutuwar wadannan mutanen, ko kuma menene ya same su.

Yace shawarar su ita ce fidda gawarwakin, amma kuma ya rage ga mahukuntar kasar su dauki matakin da suke ganin ya dace domin kauda jita-jitan da ake yayatawa game da mutuwar wadannan mutanen.

Domin daya daga cikin jita-jitan da ake yayatawa shine da yawan wadanda aka binne din an kashe su ne lokacin da suka yi zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin kasar,

Abinda mahukuntar kasar suka karyata nan take, suka ce binne mutane da yawa ba sabon al’ada bace a kasar domin rashin wadataccen makabarta.

Sai dai Prime Minista Augustin Matata Ponyoya shaidawa kanfanin dillacin labaran kasar faransa cewa binne mutanen da yawa haka na iya zamewa kuskeren jamiaan gwamnati amma wannan ba wani abin damuwa bane.

XS
SM
MD
LG